Ibrahim Musa kallah

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Mannir Yakubu FNIQS ya karbi bakuncin tawagar al’ummar garin Radda garin su sabon zababben Gwamnan Jihar Katsina Dr. Dikko Radda yau litinin a gidan shi dake tsohuwar fadar Gwamnatin Jihar Katsina Barda House.

Ziyarar nada nufin mika Godiyar ban girma ga Mataimakin Gwamnan bisa kokari da dagewa da goyama sabon Gwamnan Jihar Katsina baya da ya kasance Dan su kuma Dan uwan su.

A Jawabin Jagoran tawagar Dr. Sadik Radda ya yayi jinjina da yaba ma Mataimakin Gwamnan bisa dagewa wurin goyama Sabon Gwamnan baya tun bayan zaben fitar da gwani da ya kasance a cikin masu nema Allah da Allah bai bashi ba kuma baiyi jayayyae ba.

Dr. Sadik Radda yace kowa ya sheda yadda Mataimakin Gwamna ya jajirce wurin samun nasarar Dr Dikko Radda ko shi keep takarar sai haka.

Tun farko a na shi Jawabin Mataimakin Gwamna yayi Godiya ga yan tawagar bisa ziyarar da suka kawo mashi tare da yin kira agare su da su dage da taya Sabon Gwamnan Jihar Katsina da addu’o’in samun nasarar Jagoranci da kuma fatan alheri.

Mataimakin Gwamnan yace suna da tabbacin Dr. Dikko Radda mutum ne mai kokari wurin aiki tukuru domin sunyiw aiki tare sun san kokarin shi, kuma suna mashi fatan Allah ya bashi ikon yin ayyukan alheri fiye da wadanda akayi a halin yanzu.

Alh Mannir Yakubu yayi masu addu’ar Allah ya maida su gidajen su lafiya Allah ya kara albarka ga Jihar Katsina amiin.

Leave a Reply